| TARIHIN RAYUWATA An haifeni a garin Rigachikun (wani kauye a cikin karamar hukumar Igabi, cikin jihar Kaduna) ranar tara ga watan disamba, alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar (9th December, 1985). Gwagwarmayar Karatu Na fara karatun boko a makarantar firamarre ta garin Rigacikun (wato) "LEA Primary School Rigachikun". Na fara karatun ne ina da shekara bakwai da haihuwa (wato 1992). Na kammala karatuna na firamare ne a cikin wannan makarantar a shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da takwas (1998) A shekara ta alif dubu daya da casai'n da shida (1996) na sami shiga makarantar 'Madrasatul Tahfizil Qur'anil Kareem Rigachikun' ; makarantar islamiyya, inda a ciki ne na fara karatun addinin musulunci. Na shafe shekaru shidda (6 years) a cikin makarantar sannan kuma na kammala a shekarar alif dubu biyu da biyu (2002). Bugu da kari, na cigaba da karatun addini a gurin malamai daban-daban. Kafin nan, A shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da takwas (1998) wato bayan kammala karatun firamare, na sami shiga karamar makarantar sakandare (wato 'Government Junior Secondary School Rigachikun') .Na kammala karatun ne a cikin wannan makarantar a shekara ta alif dubu biyu da daya (2001). A shekarar dubu biyu da daya ne (wato bayan kammala karatun karamar sakandare) na samu nasarar shiga babban makarantar sakandare (wato 'Government Senior Secondary School Rigachikun'). Na kammala karatun ne a shekara ta alif dubu biyu da hudu (2004). Bugu da kari, a shekarar dubu biyu da hudun ne (wato shekarar karke da nayi a wannan makarantar), kungiyar dalibai musulmai (wato Muslim Students' Society-MSS) ta zabe ni a matsayin kakakin ta (wato 'Public Ralations Officer'-PRO). Harwa yau, a cikin shekarar ne hukumar makarantar ta zabe ni a matsyin mataimakin shugaban dalibai ( wato 'Deputy Head-boy'). A kowane bangare na sami takardar girmamawa (wato Certificate of honor). A shekarar alif dubu biyu da hudu (2004), na sami nasarar shiga makarantar koyon na'ura mai kwakwalwa (wato Computer) a makaranta mai suna 'Dinine Tech. Computer Institute'. Na fara ne a ranar bakwai ga watan uku, alif dubu biyu da biyar (7th March, 2005) sannan na kammala a ranar talatin ga watan bakwai alif dubu biyu da biyar (30th July 2005) Kwasa-kwasai A shekarar dubu biyu da uku (2003), na halarci kwas mai suna 'Leadership Training Program (LTP)'. Manufar kwas din shine horar da matasa yadda zasu zamo shuwagabanni na gari. Wadan da suka tsara kwas din sune Muslim Students' Soctiety Kaduna state area unit. Kwas din an yi shi ne a sansanin alhazai (Hajj Camp) da ke Mando Kaduna. Bugu da kari, a shekarar alif dubu biyu da hudu (2004), na sami halartar wani kwas din a jihar Zamfara. Sunan kwas din shine 'Islamic Vacation Course (IVC)'. Manufar kwas din shie zaburar da matasa don tunkarar kalubalan da suke fuskanta. An yi ma kwas din take da 'Muslim Youth and the Challenges of the 21st century'. A shekarar dubu biyu da biyar (2005), na halarci wani kwas a bangaren na'ura mai kwakwalwa (wato Computer Operation). Daga cikin darussan da na karanta harda Internet. Aikace-aikace na A halin yanzu ina aiki da wata makarantar Islamiyya mai suna 'Muhammad Jallo Foundation Islamic School Rigachikun' a matsyin mai karban kudin makaranta (school fees). Har ila yau, ina aiki a wurin a matsayin mai karantarwa. Na fara ne daga 15th/12/2002. Harwayau, na yi aiki da wata kamfani mai suna 'Divine Tech. Computers and Communications LTD'. Na yi aiki a wurin ne a matsayin malami a bangaren karantar da na'ura mai kwakwalwa. Na fara ne daga 1/2/2006. Turanci |
| My Resume |
| My Resume |
| My Resume |
| My Resume |
| My Resume |
| My Resume |
![]() |