JAKADIYA
UWAR
ISAR DA SAKONKU!
Jakadiya kurwar
na’ura mai kwakwalwa (Software) da Kamfanin Gwani Software Nigeria limited ya
tsara musamman don al-ummar Hausawa masu sha’awar aika sako ta sheqar sadarwa
da a ka fi sani da E-Mail.
Wannan yayi na 1.0 a na
iya samunsa a sheqar mu watau www.geocities.com/gwanisoftware/
ko a iya sayenta daga wannan Kamfani.
Mecece
Jakadiya?
Meye fa’idar aiki da Jakadiya
Yaya
ake aiki da Jakadiya?
Mecece
dangantakar Jakadiya da Tambari?
Meye
bambamcin Jakadiya da ke shekar Gwani Software da wadda a ke saya a faifai?
In
na sami tangarda?
Jakadiya an tsara ta ne don aika wasikunku ta sheqar Internet, ba tare da kasancewar sai an mallaki akwatin tara wasiku da aikasu ba (E-Mail account). Jakadiya kan tura wasikunku ga ‘yan uwa da abokan arziki ta sheqar Internet zuwa ga akwatunan wasiqar sheqarsu.
Za ku iya cin moriyar aiki da Jakadiya ta wadannan hanyoyi:
1. Jakadiya a na amfani da ita cikin harshen Hausa, wannan dama ce da zaku iya aika sakonku cikin harshen Hausa.
2. A iya amfani da Jakadiya ba lalle sai an mallaki akwatin tara wasiku da aikasu da suke cikin sheqar kamfanonin da a ka tanada don yin haka ba. Abin da kawai za a yi shine a shigo cikin sheqar mu a bude shafin Jakadiya, ko a sayi Jakadiya cikin faifai, sai kawai rubuta wasiqa da aika ta.
3. Jakadiya bata cin fili mai yawa cikin na’urarka mai kwakwalwa, koma bayan sauran kurwar aika wasika.
4. Jakadiya kan adana adireshin mai aiki da ita cikin shafi na musamman a sheqar mu, ta yadda duk mai neman wannan adireshi zai iya gani ta hanyar bude wannan shafi.
5. Za a iya turo da shawarwari game da yadda Jakadiya ke aiwaitar da aikinta.
Da shiga Jakadiya ga abubuwan da za a yi don aika sako:
Jakadiya dai ana amfani da ita ne kyauta a cikin sheqarmu kuma ko ba a mallaki akwatin tara wasiqu ba. Amma Tambari shi hanyar mallakar akwati ne na musamman don tara wasiqu da aika su ta sheqar Internet, a cikin wannan sheqar tamu. Tambari na nan tafe shima Kamar Jakadiya ya kasu gida biyu, akwai wanda za a iya amfani da shi kyauta har na tsawon watanni uku. Akwai wanda sayansa za’a yi ayi ta amfani da shi har zuwa lokacin da a ke so. Tambarari na nan fitowa, sai a saurari fitowarsa a wannan sheqa tamu.
Jakadiya da ke cikin wannan sheqa tamu, kyauta ake aiki da ita. Amma wadda ke cikin faifai wadda za ka iya sa ta a cikin na’urarka mai kwakwalwa ita sayanta a ke yi. Ita ta faifai an mata ‘yan tsare-tsare don ta iya aiki a cikin na’ura mai kwakwalwa. Amma wajen aiki, duk aikinsu daya ne.
In an sami tangarda a wajen aiki da
Jakadiya sai a tuntube mu ta adireshinmu [email protected]
In Jakadiyarka a faifai ta zo, to akwai hanyar samun qarin bayani cikinta. In kuma a wannan sheqar take, to a iya turo mana tambaya ta adireshinmu.
Madallah,
Mun gode.