RECORDS OF SOME OF OUR STAFF

Wasu daga cikin Ma'aikatan wannan kamfani namu sune:

Qadi Abubakar Muhammad

An haife Shi a cikin garin Bauchi (Nigeria), kuma yayi karatun digirinsa na Computer Science a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke cikin garin Bauchi. A halin yanzu yana karatun PGD a computer science a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke cikin garin Bauchi. Shine shugaban kamfani a halin yanzu.

Malam Auwal Dauda Kurawa

Haifaffen cikin garin Kano (Nigeria) ne, kuma yayi karatun diplomar shekara hudunsa a Computer science a cikin Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke cikin garin Bauchi. A halin yanzu yana karatun Digirinsa. Yana matsayin Director Engineering na wannan kamfani.

Malam Muhammad Idris

Haifaffen cikin garin Rabi Katagum(LGA a jihar Bauchi ) (Nigeria) ne, kuma yayi karatun diplomar sa a Computer science a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke cikin garin Bauchi, a halin yanzu yana cigaba da karatunsa a wannan Jami'a. Malam Muhammad yana da aure har da 'ya'ya uku a halin yanzu. Yana matsayin Director sales na wannan kamfani.

Malam Al-Amin Abubakar Saraki

Haifaffen cikin garin Bauchi (Nigeria) ne, kuma yayi karatun diplomar sa a Computer science a Institute of Management & Computer Studies da ke cikin garin Bauchi, a halin yanzu yana cigaba da karatunsa. Yana matsayin Director Training na wannan kamfani.

St. Christy O. Diagi,da

An haife ta a cikin jihar Edo (Nigeria). Ta sami karamar difloma (OND) a Accounting daga kwalejin kimiyya da fasaha na gwamnati tarayya (Fedaral Polytechnic) da ke cikin garin Bauchi.A halin yanzu dai tana cigaba da karatun babbar difloma (HND) a wannan makaranta da ke cikin garin Bauchi. Kuma itace cashier(ma'ajiyi) din wannan kamfani.

Mercy C. Diagi.

An haife ta a cikin jihar Edo (Nigeria). Ta yi karatun MS Office XP and Internet Operation a cibiyar bincike ta Farfesa Iya Abubakar, karkashin jagoranci Kasar Amurka, da ke nan cikin garin Bauchi.  A halin yanzu dai tana cigaba da karatun karamar difloma a kwalejin kimiyya da fasaha na gwamnatin tarayya (Federal Polytechnic) da ke cikin garin Bauchi. Ita ma maikaciya ce a wannan kamfani.

 

WASIKA ZUWA GA MA'AIKATANMU

Adireshin ka/ki

Zuwa ga

Wasikarka/ki a nan

Register your domain name and build your site at UNI.CC
Hosted by www.Geocities.ws

1